WANI LIKITA A NAN KANO YA YI KIRA GA AL’UMMA DA SU RINKA ZIYARTAR AASIBITI DON DUBA LAFIYAR IDANUN SU A KAN LOKACI

Wani kwararren Likitan bangaren Idanu a Asibitin kwararrun na Murtala Muhammad a nan Kano, Dakta Usman Mijinyawa, ya yi kira ga al’umma da su rinka ziyartar Asibiti don duba lafiyar idanun su a kan lokaci, ba wai sai sun sami matsala da ta jibanci idanun su ba.
Dakta Usman Mijinyawa ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala a wani bangare na bikin ranar Gani ta Duniya da ya gudana a jiya.
Ya ce, wajibi ne kowane mutum ya rinka ziyartar Asibiti domin duba Lafiyar sa, ko da kuwa sau daya ne a shekara, bawai sai ciwo ya kamashi ba.

Dakta Usman Mijinyawa, ya kuma ce duba marasa lafiya kyauta ne a Asibitoci, a don haka ya yi kira ga al’umma su rinka halartar Asibiti don duba lafiyar su a kan kari.

en_USEnglish
en_USEnglish