AL’UMMAR ROGO NA KORAFI GAME DA ABABEN MORE RAYUWA

Al’ummar garuruwan Ruwan Bago,Tsara da Gwangwan a Karamar Hukumar Rogo dake nan Kano sun koka bisa rashin hanya da sauran ababen more rayuwa.
Tawagar mazauna garuruwan uku sun koka ne lokacin da suka ziyarci Ma’aikatar raya Karkara don mika takardar koken ga gwamnati dan nema dauki game da halin da suke ciki na rashin hanya.
Da yake jawabi a madadin mazauna yankunan Tijjani Sanusi Ruwan Bago, yace rashin hanyar na shafar karatun yayansu da ma harkokinsu na Ibada.

A nasa jawabin Kwamishinan raya karkara na jihar kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce gwamnati ta karbi koken su kuma za ta magance matsalar.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewar mazauna Garuruwan na Ruwan Bago, dakuma Gwan-gwan a Karamar Hukumar ta Rogo na fatan samun dauki daga Gwamnati da Kungiyoyin tallafawa Alumma.

en_USEnglish
en_USEnglish