AN JA HANKALIN AL’UMMA DA SU RINKA KULA DA TSAFTAR JIKI DA KUMA MUHALLIN SU

Sarkin tsaftar Kano, Alh Jafar Ahmad Gwarzo ja hankalin al’umma da su rinka kula da tsaftar jiki da kuma muhallin su, kasancewar kowacce ta na farawa ne da rashin tsafta.
Jafar Ahmad Gwarzo,, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin shari’a a aikace na nan gidan rediyon Dala.
Ya ce duk wasu cututtuka ana samun su ne ta rashin kula da tsafta wanda hakan ya sa cutar ke samun gurbi a jikin dan Adam yayin da aka yi watsi da ita.

Ya kuma kara da cewar hanyar amfani da kofin shan ruwa ga mutane sama da biyu na daya daga cikin hanyar kamuwa da cututtuka masu yaduwa.

Haka zalika, sarkin tsaftar jihar Kano, Jafar Ahmad Gwarzo, ya kuma shawarci al’umma da su rinka wanke hannun su yayin da suka gaisa da al’umma musamman a lokutan da zasu kai abu bakin su.

en_USEnglish
en_USEnglish