GWAMNATIN KANO TA SHA ALWASHIN SAMAR DA SHUGABAN KASUWANNI A GWAMNATANCE

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin samar da shugaban kasuwanni a gwamnatance, a kowace kasuwa da ke fadin jihar nan, kamar yadda akayiwa kasuwar sabon gari.
Hakan ya fito ne ta bakin kwamishinan kasuwanci na jihar kano Alhaji Ahmad Rabi’u, a wani taro da manema labarai da ya gudanar a ofishin sa.
Ya ce ta haka ne kawai za’a magance duk wani rikici da yake damun kasuwannin da ke fadin jihar nan.

Ya kuma ce tuni shirye-shirye sunyi nisa don samar da wata kasuwar baja-kolin fulawa a garin Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewar, kwamishinan ya bayyana cewa, kawo yanzu gwamnatin jihar kano ta ka she makudan kudade don samar wa da matasa aikin yi a fadin jihar nan.

en_USEnglish
en_USEnglish