KWALEJIN SA’ADATU RIMI ZATA BADA KULAWA GA HARKOKIN WASANNI

Shugaban kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke nan Kano, Dakta Isah Yahya Bunkure, ya ce babban abin da yasa a gaba, shi ne tallafawa matasa ta bangaren wasanni, don kawo cigaba tare da hada kan matasan baki daya.

Dakta Isah Yahaya Bunkure, ya bayyana hakan ne, ta cikin wata sanarwa mai kunshe da sa hannun jami’ar hulda da jama’a ta kwalejin, Malama Amina Abdul’aziz Abba, lokacin da ya ke karbar bakuncin mambobin kungiyar Greater Tomorrow Academy.
Bunkure ya kuma ya bawa gwamnati Jihar Kano, bisa tallafawa matasa da ta ke yi wajen harkar kwallon kafa, tare da kokarin ciyar da matasa gaba.
A nasa jawabin shugaban kungiyar, Greater Tomorrow, Malam Umar Bashir godewa kwalejin ya yi bisa kokarin ta na tallafawa matasa a harkokin wasanni da kuma bangarori da dama don cigaban matasan.

en_USEnglish
en_USEnglish