AN YI KIRA GA MATASA DA SU RINKA TUNANIN ABUBUWAN DA ZA SU AIKATA KAFIN AIWATAR DA SHI

Wani mai rajin inganta rayuwar matasa a nan kano kwamred Bello Basi, ya yi kira ga matasa da su rinka tunanin abubuwan da za su aikata kafin aiwatar da shi, musamman a wannan lokaci da muke ciki.
Kwamred Bello Basi ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin wannan rayuwa na nan gidan rediyon Dala.
Ya ce a irin wannan lokaci da muke ciki a kwai bukatar matasa su rinka tunanin menene mafi kyau a cikin rayuwar su.

Ya kara da cewa wajibi ne malamai su ji tsoron A…. su rinka fadawa shugabanni gaskiya.

Kwamred Bello Basi, ya kuma bukaci iyaye da su rinka lura da tarbiyyar ‘ya’yan su musamman a wannnan lokaci da matasa ke tsunduma harkokin bangar siyasa.

en_USEnglish
en_USEnglish