RUNDUNAR ‘YAN SANDA TA KANO TA GARGADI JAMI’ANTA A KAN DAUKAR MAKAMAI A HANNU

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gargadi Jami’anta da su guji daukar makamai a hannu wadanda suka saba dokar runduunar yayin da suke bakin aiki.
Kakakin rundunar a nan kano SP Magaji Musa Majiya ne ya bayyyana hakan, jim kadan bayan kammala shirin Dansanda da Jama’a na nan gidan rediyon Dala da ya gudana a jiya.
Ya ce, duba da yadda masu laifi ke amfani da irin makaman da basu kamata ba, yasa su ke kira ga Jami’an su da su kaucewa amfani da irin wadannan makaman.
TRACK UP
Magaji Musa Majiya ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Kano da su cigaba da basu hadin kai yayin gudanar da ayyukan su na tsaron rayuka da dukiyar al’umma kamar yadda suka saba.

en_USEnglish
en_USEnglish