BABBAR KOTUN TARAYYA , TA YANKEWA MAI RAKUMI, HUKUNCIN DAURIN SHEKARU 10 A GIDAN KURKUKU

Comments are closed

Babbar kotun tarayya dake zaman ta a nan Kano, ta yankewa Malam Abubakar Ishaq wanda aka fi sa ni da suna Mai Rakumi, hukuncin daurin shekaru 10 a gidan kurkuku sakamakon samun sa da dalifin buga kudade na jabu ta hanyar tsubu.
Tun da fari dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, it ace ta karbi mai Rakumi daga hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, bayan damke shi a gidan sa yayin wani simame da aka same si da dalar Amurka 176 na jabu.
Bayan amsa wasu tambayoyi daga hukumar a wancan lokacin, hukumar EFCC ta bada belin sa, sai dai kuma daga baya ne ta gurfanar da shi a gaban kotun tarayya dake nan Kano.
Mai rakumi ya kuma amsa laifuka biyu da ake zargin sa dasu, wanda aka dage zamanta zuwa Alhamis.
A yayin zaman kotun na jiya, mai shari’a Luis Alogwa, ya yanke hukuncin daurin shekaru biyar biyar a kowane laifi guda da ake tuhuman sa, yanzu haka dai Mai Rakumi zai shafe tsawon shekara 10 a gidan kurkuku.

Comments are closed.