AN BUKACI YAN SIYASA DA SU GUJI CIN HANCI DA RASHAWA

Comments are closed

Dan takarar majalisar tarayya a jam’iyyar Legacy Party of Nigeria LPN, Mahammad Sautil Haq, yayi kira ga ‘yansiyasa da su guji cin hanci da rashawa, domin tsaftatacciyar rayuwa.

Sautil haq, yayi kiran ne yayin da ya gabatar da jawabi a ofishin sa da ke unguwa uku.

”Ya ce ba karamin koma baya cin hanci da rashawa ke haifarwa ba acikin al’umma, inda a yanzu babu wani abu da ake yi a tsakanin al’umma ba tare da cin hancin ya gilma ba, koda kuwa shugabanni ne masu rike da madafun iko”’.

”Ya kara da cewa, karamar hukumar kumbotso tana daya daga cikin kananan hukumomin da suke bada gudunmawa a kano, sannan tana daga cikin kananan hukumomi da su ke koma baya a fannin samun ababen more rayuwa”.

 

Comments are closed.