SHUGABAN KASA YACE ZAI DAUKI MATAKI A KAN GWAMNAN JIHAR KANO

Comments are closed

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zasu dau matakin da ya dace, akan zargin da akewa gwamnan kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na karbar na goro a hannun ‘yan kwangila.

Shugaba Buhari ya tabbatar da hakan ne lokacin da wani dalibi dan asalin jihar kano da ke karatu a kasar faransa ya kalubalanci gwamnatin tarayya kan ta yi koyi da gwamnan kano wajen biyan dalibai tallafin karatu da sauran su.

”Ya ce yanzu haka sun mika kwafin faifan hoton bidyon ga Jami’an tsaro don bincike akan sa tare da sahihancin faifan bidiyon, kuma zasu dauki matakin da ya dace matukar aka sami wanda ake zargi da laifin”.

Sai dai wasu daga cikin makusantan shugaban kasa basu ji dadin furucin shugaban kasa ba, ciki kuwa akwai, wakilin Nassarawa Nasir Ali Ahmed, da kuma mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yada labarai Sha’aban Ibrahim Sharada, wanda suka roki ‘yan jaridu da kada su yada labarin.

 

 

Comments are closed.