GWAMNATIN JIHAR KANO ZA TA KASHE SAMA DA NAIRA BILIYAN 26 WAJEN BUNKASA HARKOKIN SAMAR DA RUWAN SHA A FADIN JIHAR

Gwamnatin jihar kano za ta kashe sama da naira biliyan 26 wajen bunkasa harkokin samar da ruwan Sha a fadin jihar nan.
Gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin gabatar da kunshin kasafin kudin badi a zauren majalisar dokokin jihar kano da safiyar yau Laraba.
Yace duba da mahimmancin da ruwan Sha ke dashi, shi ya sa gwamnatin kano ta ware makudan kudi don bunkasa bangaren na ruwan sha.
Gwamnan Kano ya kuma ce a cikin kasafin kudin na badi gwamnatin sa zata kashe sama da naira biliyan biyu da kuma miliyan biyu da dari takwas wajen bunkasa harkokin tsaro a jihar.
Kasafin kammala jawabin nasa gwamnan kano yayi kira ga matasan jihar nan, dasu guji barin ‘yan siyasa na amfani da su cikin bangar siyasa.
Wakiliyar mu a majalisa, Khadija Ishaq Muhammad ta ruwaito cewa gwamnan ya gabatar da kunshin kasafin na sama da naira biliyan dari biyu da goma sha tara, yayin da bangaren manyan ayyuka ya samu sama da naira biliyan dari da talatin da shida.

en_USEnglish
en_USEnglish