A RINKA BUDE MAKARANTUN DOMIN KARANTAR DA MASU LAIFI

Comments are closed

Kwamandan Hisba na karamar hukumar Gwale anan kano Alhaji Yahaya Bala Sabon Sara, ya bukaci gwamnati da ma masu hannu da shuni da su rinka bude wasu makarantu domin karantar da masu laifi.

Alhaji Yahya Bala ya yi wannan kiran ne yayin wata ziyara da ya kai ofishin ‘yan bijilante na ja`en layin gidan Dagaci a jiya.

Ya ce”idan har za’a samar da irin wadannan makarantu to babu makawa sai an kawo karshen aikata laifuka a unguwannin jihar nan”.

A nasa bangaren jagoran kwamitin tsaro na unguwar ja`en Alhaji Isa Musa Sharada cewa yayi suna da kwamitin da yake wayarwa da masu laifuka kai.

Wakilin gidan radion dala ya rawaito cewa al’umma da dama ne dai suka halarci taron ciki kuwa har da mambobin kungiyar Bijlanten yankin.

Comments are closed.