YAWAN SHAN RUWA DA YAWAN YIN FITSARI NA DAGA CIKIN ALAMUN CIWON SIGA

Wani kwararren Likitan cutar diabetes wanda aka fi sani da ciwon siga a Asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake nan kano, Dakta Abubakar Usman, ya bayyana yawan shan ruwa da yawan yin fitsari da rama da dai sauran wasu alamu, cewa na daga cikin alamun ciwon siga.
Likitan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin Mu tambayi likita na nan gidan rediyon Dala da ya gudana a yammacin jiya.
Ya ce da zarar mutum yaji irin wadannan alamu, yayi kokarin zuwa asibiti don duba lafiyar sa.

Ya kuma kara da cewa, duk wanda yasan a danginsu a kwai masu irin wannan ciwo, ya kai shekaru 35 zuwa 40 kamata yayi ya rinka ziyartar asibiti.

Dakta Abubakar Usman ya kuma ja hankalin al’umma da su rinka motsa jikin su domin kaucewa kamuwa da cutar siga.

en_USEnglish
en_USEnglish