AN BAYYANA MARIGAYI SARKIN KANO DAKTA ADO BAYERO A MATSAYIN MUTUM MAI JAJIRCEWA WAJEN HIDIMTAWA MARASA KARFI DA ADDININ MUSULUNCI

Wani malami a nan kano Malam Sagir Garba Kutuga, ya bayyana marigayi sarkin kano Dakta Ado Bayero a matsayin mutum mai jajircewa wajen taimakawa marasa karfi, da kuma addinin musulunci.
Malam sagir kutuga ya bayyana hakan ne, yayin bikin mauludin da kungiyar tunawa da Marigayi mai martaba sarkin kano Dakta Ado Bayero wanda ya gudana a gidan sa dake Gandu.
Ya ce son manzon A…. na sanya farin ciki da nishadi a zukatan al’umma tare da yin koyi da halayen sa.

Da yake nasa jawabin limamin masallacin juma’a na Dala, sheik Albukar Yusif Makwarari, jan hankalin mutane yayi da su yawaita ambaton Al.. domin yana sanya nutsuwa a zukata.

Wakiliyar mu Madina Shehu Hausawa ta rawaito cewa, Hakimai da dama ne dai suka halarci taron mauludin, tare da manyan malamai daga sassa daban daban.

en_USEnglish
en_USEnglish