AN BUKACI AL’UMMA DA SU RINKA TALLAFAWA MARAYU DA MARASA KARFI

Malamin addinin musulunci Malam Ibrahim Khalil ya bukaci al’umma da su rinka tallafawa marayu da marasa karfi, domin a gudu tare a kuma tsira tare.
Malam Ibrahim Khalil ya fadi hakan ne yayin bikin saukar karatun alqur’ani mai girma na makarantar Waya Islamiyya da ke Ja’en a karamar hukumar Gwale.
Ya ce duba da yadda wasu daga cikin al’umma ke bukatar taimako yasa suke kira da a rinka tallafawa marasa karfi.
TRACK UP
A nasa jawabin shugaban makarantar Malam Rabi’u Jibril kira yayi ga iyaye da su tashi tsaye wajen baiwa ‘ya’yan su ilimin addini.
TRACK UP
Wakilin mu Auwal Hamza Ibrahim ya rawaito cewa Dalibai 13 ne suka gudanar da saukar ciki akwai maza 5 mata 8.

en_USEnglish
en_USEnglish