MAJALISAR DATTAWA TA SHIRYA ZAMA NA MUSAMMAN DON TATTAUNAWA AKAN YADDA ‘YAN SIYASA KE SIYEN KURI’U A HANNUN MASU ZABE

Majalisar Dattawan Kasar nan ta shirya wani zama na musamman don tattaunawa akan yadda wasu ‘yan siyasa ke siyen kuri’u a hannun masu zabe a lokutan zabe.
Majalisar dai ta shirya zaman jin bahasin ne sakamakon yadda a wasu zabukan da aka gudanar a baya-bayan nan a wasu sassan kasar nan, aka rinka samun rahotannin siyar da kuri’u a rumfunar zabe.
Sanata Suleman Nazifi shi ne shugaban kwamitin, ya ce babban abin da yasa majalisar za ta zauna shi ne yadda za’ayi, a kaucewa siyen kuri’u a zabukan badi.

Ya kuma kara da cewa wasu daga cikin ‘yan siyasa na zuwa rumfunar zabe suna rabawa masu zabe wasu kayayyaki, wanda ya ce hakan abin takaici ne.

Sanata Suleman Nazifi, ya kuma yi kira ga masu kada kuri’a da ka da su yarda su sayar da kuri’un su, domin da ita ne kadai zasu zabi mutumin da ya cancanta.

en_USEnglish
en_USEnglish