ALKALIN MAJESTRATE NA DA HURUMIN SAUYAWA SHARI’A KOTU ZUWA NA ADDININ MUSULUNCI

Kakakin kotunan jihar kano Baba Jibo Ibrahim ya bayyana cewa, alkalan majestrate na da hurumin sauyawa shari’a kotu zuwa na addinin musulunci, amma kafin su fara saurarar karar.

Baba Jibo ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin shari’a a aikace na nan gidan rediyon Dala.

Ya ce dukkan alkalan majestrate nada damar sauyawa kara kotu matukar basu fara sauraron shari’ar ba.

Ya kara da cewa alkalan majestrate basu da damar sauyawa kara kotu matukar daga babbar kotun jiha take.

Baba jibo Ibrahim ya kuma ce alkalai na da damar sauyawa kara kotu matukar akwai wani kusanci tsakanin alkali da mai kara ko kuma wanda a ke kara.

en_USEnglish
en_USEnglish