AL’UMMAR YANKIN UNGUWAR SABUWAR GANDU SUN YABAWA GWAMNATIN JIHA BISA YADDA TAKE GUDANANR DA AIKIN TITI A YANKIN

Al’ummar yankin unguwar Sabuwar Gandu dake karamar hukumar Kumbotso sun yabawa gwamnatin jihar Kano bisa yadda take gudanar da aikin titin kwalta a yankin na Sabuwar Gandu.

Mazauna yankin sun ai bayyana hakan ne ta bakin guda daga cikin su, Malam Muhammd Ahmad a yayin ziyarar duba aikin shimfida kwalta da wakilin mu na Zazu yakai yankin.

Ya ce, kamata yayi gwamnatin da ta sake dage damtse wajen shimfida ayukan alheri a kowane unguwanni dake fadin jihar nan.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da aikin ya shafa, dasu saka idanu wajen kula da wajen gyara titunan nasu dama magudanan ruwa.

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito mana cewa, yanzu haka aikin shimfida kwaltar yayi nisa a yankin na Sabuwar Gandu.

en_USEnglish
en_USEnglish