AN BUKACI GWAMNATI DA TA SAMI WADATACCEN WURIN AJIYE MASU LAIFI

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano NDLEA, Dakta Ibrahim Abdul, ya bukaci gwamnati da ta samar da wadataccen wurin ajiye masu laifi, ta yadda zai kasance wurin maza daban na mata daban.

Dakta Ibrahim Abdul, ya yi wannan kiran ne yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala da safiyar yau.

Ya ce duba da yadda korafe-korafe yayi yawa daga masu kawo ‘ya’yan su don a tarbiyyartar da su yasa suke kira da a samar musu da wurin.

Ya kuma ce dole sai al’umma sun taimaka wajen dakile ta’ammali da miyagun kwayoyin, kana za’a samu daidaito.

Dakta Ibrahim Abdul ya kuma ce kalubalen da hukumar ke fuskanta shi ne karancin ma’aikata da kuma samun bayanan sirri daga jama’ar gari.

en_USEnglish
en_USEnglish