AN KARRAMA ‘YAN ZAZU NA GIDAN REDIYON DALA

Kungiyar Dalibai ‘yan asalin jihar kano reshen kwalejin nazarin addinin muslunci da harkokin shari’a ta Legal, sun karrama ‘yan zazu na nan gidan rediyon Dala, bisa jajircewar su wajen kawo abin da ke faruwa kai tsaye a fadin jihar kano.

Yayin karrama mashahuran mutane da ke bada gudunmawa wajen cigaban rayuwar al’umma, taron dai ya gudana ne a kwalejin ta marigayi malam Aminu Kano da ke kan titin zuwa tsohuwar jami’ar bayero da ke nan kano.

Shugaban kungiyar Daliban, Kwamrade Nuhu Sani, ya ce sun karrama ‘yan zazun ne da sauran mutane don karfafa musu gwiwa wajen cigaba da hidimtawa al’umma da kuma ciyar da kasa gaba.

A nata jawabin mataimakiyar shugabar makarantar Legal, Barista Dija Isah Hashim, ta kuma yabawa daliban bisa yadda suka fito da irin al’adun gargajiya a cikinn kwalejin.

Wakilin mu Tijjani Adam, ya kuma rawaito mana cewa, mataimakiyar shugabar makarantar, Barista Dija Isah Hashim, ta kuma yi kira ga daliban dasu gujewa satar jarabawa a cikin kwalejin.

en_USEnglish
en_USEnglish