KUNGIYAR MASU SANA’AR RINI SUN BUKACI MATASA DA SU RUNGUNMI SANA’A MAIMAKON SHIGA BANGAR SIYASA

Kungiyar masu sana’ar rini dake yankin unguwar Samegu a karamar hukumar Gwale a nan Kano sun bukaci matasa da su guji shiga bangar siyasa maimakon hakan da su rungumi sana’o’in dogaro dakai.

Shugaban kungiyar marunan, Abubakar Sadik Sa’ad shine ya yi wannan kiran yayin ganawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu a yau.

Ya ce kamata yayi matasa da su nemi sana’a maimakon shiga bangar siyasa musamman ma a wannan lokaci.

Abubakar Sadik, ya kuma ce “duk kankantar sana’a matasa su ringumeta hannu bibiyu.”

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito mana cewa, kimanin matasa sama da 50 ne daga unguwanni daban-daban ke gudanar da sana’ar rini, wanda kuma kungiyar ta ce kofa abude take ga duk wani matasahi da yake sha’awar shiga sana’ar ta rini.

en_USEnglish
en_USEnglish