AN BAYYANA RASHIN RIKO DA KOYARWAR MA’AIKI A MATSAYIN ABUN DA YA SABBABA LALACEWAR MATASA A WANNAN ZAMANI

Wani malamin addinin musulinci a nan kano malam Musa Sidi Ibrahim, ya bayyana rashin riko da koyarwar ma’aiki S.A.W. a matsayin abun da ya sabbaba lalacewar matasa a wanan zamani.

Malam Musa Sidi ya bayyana hakanne, a wani taron maulidi daya gudana a unguwar Ajawa dake karamar hukumar gwale.

Ya kuma kara da cewa su matasa suna bukatar a jasu a jiki tare da dabbaka kyawawan halaye ta yadda zasu yi koyi.

A nasa jawabin jagoran gudanar da maulidin, malam Kabiru Abdussalam, y ace kamata ya yi malamai sun rinka gabatar da jawaban fadakar da al,umma kan halayen ma’aiki da suka zo cikin litattafan gabata, don ganin an dora su akan hanyar shiriya.

Wakilinmu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa malamai da dama ne suka gabatar da jwabai a yayin taron maulidin.

en_USEnglish
en_USEnglish