Monthly Archives: February 2019

An ja hankalin al’umma da su rinka karanta alqur’ani mai girma.

Comments are closed
Limamin Masallacin juma’a na Usman bin Affan dake unguwar Gadon Kaya, malam Abdallah Usman Gadon kaya, ya ja hankalin al’umma da su rinka baiwa karatun alqur’ani muhimmanci. Malam Abdallah Gadon kaya ya yi wannan jan hankalin ne, jim kadan bayan kammala shirin rayuwa abar koyi na nan gidan rediyon Dala. Ya ce ''sau da dama al’umma su
more

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama wata babbar mota, makare da miyagun kwayoyi sama da kala 10, da kuma duro 12 na madarar sukudayin.

Comments are closed
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama wata babbar mota, makare da miyagun kwayoyi sama da kala 10, da kuma duro 12 na madarar sukudayin. Kwamishinan yansanda na kano CP Muhammad Wakili, shi ne yayi holin matasan da kayayyakin miyagun kwayoyin da aka kama a yammacin jiya. CP Wakili ya kuma ce, ''Rundunar ta kama wani mutum
more

An bayyana cewa kowane dan kasa na da damar yin zabe matukar yana da katin zabe

Comments are closed
Sakatariyar kungiyar Lauyoyi mata ta kasa reshen jihar Kano, kuma Malama a sashin koyar da aikin Lauya, a Jami’ar Bayero dake nan Kano, Barista Hassana Bashir, ta bayyana cewa ''kowane Dan’adam yana da ‘yancin da zaiyi zabe matukar yana da katin zabe''. Barista Hassana Bashir ta bayyana hakan ne yayin ganawar ta da wakilin gidan rediyon
more

An bukaci matasa da su kasance masu bin doka da oda yayin zaben bana.

Comments are closed
Wani mai fashin baki a kan al’amuran matasa a karamar hukumar Dala, Injiniya Auwalu Rabiu Sifikin, ya ja hankalin matasa da su guji duk wani da ka’iya kawo nakasu a zabe mai karatowa. Injiniya Auwalu ya bayyana hakan ne, yayin gudanar da taron gayyatar ‘yan takarar majalisar tarayya, wanda kungiyar Dala ina Mafita, ta shirya a
more

An yi kira ga iyaye da su rinka tallafawa makarantun islamiyya,

Comments are closed
Dagacin sharada Alhaji Ilyasu Mu’azu Sharada, ya ja hankalin iyaye da su rinka tallafawa makarantun islamiyya, kamar yadda suke mayar da hankali kan makarantun zamani. Dagacin na sharada, ya yi wannan jan hankalin ne, yayin Musabaqar karatun alqur’ani mai girma da makarantar Zaidu bin Sabit Litahfizul qur’an, ta gudanar a jiya lahadi. Ya ce ''wajibi ne sauran
more

An ja hankalin al’umma, da su mayar da hankali wajen zaben shugabanni nagari.

Comments are closed
Wata malamar addinin musulunci a nan kano, Malama Aisha Zakariyya ta ja hankalin al'umma, da su mayar da hankali wajen zaben shugabanni nagari. Malama Aisha Zakariyya, ta bayyana hakan yayin taron  wayar da kan al'umma wajen zaben shugabanni na gari, wanda ya gudana a jiya lahadi, a harabar makarantar Imamu Muslim Littahfizul kur'an da ke gwazaye. Ta
more

Karamar hukumar Dala ta bukaci iyayen yara dake yankin cewa da su ribaci tsarin allurar rigakafin polio, don kare lafiyar ‘ya’yan su.

Comments are closed
Karamar hukumar Dala ta bukaci iyayen yara dake yankin cewa da su ribaci tsarin allurar rigakafin polio, don kare lafiyar ‘ya’yan su. Mai riko mukamin shugaban karamar hukumar Dala, Ishaq Tanko Gambaga, ne yayi wannan kiran, yayin fara aiwatar da allurar a yankin a karshen makon da ya gabata. Gambaga ya kuma ya bawa jami’an da kuma
more