An bukaci matasa da su kasance masu bin doka da oda yayin zaben bana.

Comments are closed

Wani mai fashin baki a kan al’amuran matasa a karamar hukumar Dala, Injiniya Auwalu Rabiu Sifikin, ya ja hankalin matasa da su guji duk wani da ka’iya kawo nakasu a zabe mai karatowa.

Injiniya Auwalu ya bayyana hakan ne, yayin gudanar da taron gayyatar ‘yan takarar majalisar tarayya, wanda kungiyar Dala ina Mafita, ta shirya a makon jiya.

Ya ce ”kamata yayi ‘yan takara su fitar da jadawalin irin ayyukan da zasu yiwa al’umma musamman matasan yankin karamar hukumar Dala”.

Da yake jawabi shugaban kungiyar ta Dala ina Mafita, kwamred Lamin, cewa ”sun shirya domin jin matsayin matasa game da zabe mai karatowa”.

Wakilin mu Buhari Isah ya rawaito cewa, ‘yan takara shida aka gayyata amma uku daga cikin su ne kadai suka halarci tattaunawar.

Comments are closed.