An ja hankalin al’umma, da su mayar da hankali wajen zaben shugabanni nagari.

Comments are closed

Wata malamar addinin musulunci a nan kano, Malama Aisha Zakariyya ta ja hankalin al’umma, da su mayar da hankali wajen zaben shugabanni nagari.

Malama Aisha Zakariyya, ta bayyana hakan yayin taron  wayar da kan al’umma wajen zaben shugabanni na gari, wanda ya gudana a jiya lahadi, a harabar makarantar Imamu Muslim Littahfizul kur’an da ke gwazaye.

Ta ce ”samun nagartattun shugabanni masu tsoron A… shi ne zai sanya al’umma ta samu cigaba me dorewa”.

A nata bangaren, Malama Rahila Ahmad, wadda ta kasance a cikin taron, ”kira tayi ga mata da su zama masu yin shigar da ta kamata a lokutan da zasu fita domin kada kuri’unsu”.

Wakiliyarmu Zulfa’u Musa yakasai ta rawaito cewa malaman sun bukaci al’umma da su cigaba da addu’ar neman zaman lafiya da arziki me dorewa ga jiha dama kasa baki daya.

Comments are closed.