an ja hankalin al’umma musamman matasa da su kula da ‘yancinsu a lokutan zabe me karatowa.

Comments are closed

Wani masani a fannin kimiyyar siyasa da ke kwalejin share fagen Shiga jami’a ta nan Kano CAS, Kwamred Abdulkadir Jogana, ya ja hankalin al’umma musamman matasa da su kula da ‘yancinsu tare da watsi da duk wata akida da ta sabawa doka, a lokutan zabe me karatowa.

Kwamred Abdulkadir Jogana, yayi wannan kiran ne, yayin taron wayar da kai tare da bayar da tallafi, da wata kungiyar inganta rayuwar matasa mai suna Kano front, ta shirya a nan Kano.

Ya ce ”kasancewar matasa su ne kashin bayan kowace al’umma, kamata yayi su zamo jakadu na gari ta yadda za’a ayi alfahari dasu a fadin jahar nan da ma kasa baki daya”.

”Ya kuma ja hankalin al’umma da su guji sayar da kuri’un su ko karbar na goro don zabar wani Dan takara”.

Wakiliyar mu Zulfa’u Musa Yakasai ta rawaito cewa  taron ya samu halartar dalibai da dama wanda mafi yawancin su mata ne ‘yan asalin jihar nan.

Comments are closed.