An yi kira ga iyaye da su rinka tallafawa makarantun islamiyya,

Comments are closed

Dagacin sharada Alhaji Ilyasu Mu’azu Sharada, ya ja hankalin iyaye da su rinka tallafawa makarantun islamiyya, kamar yadda suke mayar da hankali kan makarantun zamani.

Dagacin na sharada, ya yi wannan jan hankalin ne, yayin Musabaqar karatun alqur’ani mai girma da makarantar Zaidu bin Sabit Litahfizul qur’an, ta gudanar a jiya lahadi.

Ya ce ”wajibi ne sauran makarantu suyi koyi da makarantar wajen shirya irin wannan musabaqar, domin bunkasa karatun alqur’ani mai girma”.

A nasa jawabin shugaban makarantar Lamin Shu’aibu Alhassan, cewa yayi ”sun shirya musabaqar ne domin zaburar da dalibai”.

Suma daliban da sukayi nasarar lashe gasar musabaqar ”sun bayyana farin cikin su, tare da kira ga sauran dalibai kan su jajirce wajen neman ilimi”.

Wakilin mu Buhari Isah ya rawaito cewa, Musabakar it ace karo na biyu da makarantar ta gudanar, an kuma raba kekunan dinki da injin taliya da keken hawa da atamfofi, ga wadanda suka samu nasara.

Comments are closed.