An ja hankalin matasa da su kara zage damtse wajen neman ilimin addinin musulunci.

Comments are closed

Dagacin Dorayi Babba, Alhaji Musa Badamasi Bello, ya ja hankalin matasa da su kara zage damtse wajen neman ilimin addinin musulunci, domin gyara rayuwar su ta duniya da kuma ta gobe kiyama.

Dagaci ya bayyana hakan ne yayin bikin saukar karatun alqur’ani mai girma na makarantar Abdullahi Bin Umar, wanda ya gudana a karshen makon da ya gabata.

Ya ce ”duba da yadda rayuwa take kasancewa a yanzu, ya zama wajibi matasa su tashi tsaye don neman ilimin addinin musulunci”.

A nasa jawabin shugaban makarantar, Malam Aminu Ibrahim,” bayyana farin cikin sa yayi bisa saukar da daliban suka yi”.

Wakilin mu Munzali Aliyu Yamadawa, ya rawaito dalibai 29 ne su ka gudanar da saukar karatun alqur’anin, ciki akwai maza 14 da kuma mata 15.

Comments are closed.