Karamar hukumar Dala ta bukaci iyayen yara dake yankin cewa da su ribaci tsarin allurar rigakafin polio, don kare lafiyar ‘ya’yan su.

Comments are closed

Karamar hukumar Dala ta bukaci iyayen yara dake yankin cewa da su ribaci tsarin allurar rigakafin polio, don kare lafiyar ‘ya’yan su.

Mai riko mukamin shugaban karamar hukumar Dala, Ishaq Tanko Gambaga, ne yayi wannan kiran, yayin fara aiwatar da allurar a yankin a karshen makon da ya gabata.

Gambaga ya kuma ya bawa jami’an da kuma masu ruwa da tsaki na bangaren lafiya a karamar hukumar ta Dala, bisa jajircewar su wajen inganta harkokin lafiyar yankin.

Da ta ke jawabi mai kula da bangaren lafiya a matakin farko na yankin, Hajiya Aishatu Sani Wali,  ta yi tsakanin kwanaki biyar da suka yi suna gudanar da aikin na Polio a yankunan karamar hukumar, sun yiwa yara sama da 120 allurar.

Comments are closed.