Masarauta ta ja hankalin sabon mai unguwa da ya kasance mai adalci

Comments are closed

Hakimin kumbotso Alhaji Ahmad Ado Bayero ya ja hankalin sabon mai unguwar Ciranci kwari, Malam Hafizu Garba Mandawari, da ya kasance mai adalci a tsakanin al’ummar da ke yankin.

Alhaji Ahmad Ado bayero, wanda ya samu wakilcin Malfa, yayi wannan jan hankalin ne yayin bikin nadin me unguwar a fadar hakimin dake karamar hukumar kumbotso.

Ya ce “wajibi ne mai unguwar ya jajirce wajen kawowa al’ummar yankin cigaba ta fannin ilimi da kuma lafiya”.

A nasa bangaren sabon mai unguwar Malam Hafizu Garba Mandawari, cewa yayi zai yi duk mai yiyuwa wajen kawo duk wasu abubuwa da zasu ciyar da yankin gaba.

Wakilin mu Buhari Isah ya rawaito cewa al’umma da dama ne suka halarci bikin nadin sabon mai unguwar ta Chranci kwari.

 

Comments are closed.