An bayyana cewa kowane dan kasa na da damar yin zabe matukar yana da katin zabe

Sakatariyar kungiyar Lauyoyi mata ta kasa reshen jihar Kano, kuma Malama a sashin koyar da aikin Lauya, a Jami’ar Bayero dake nan Kano, Barista Hassana Bashir, ta bayyana cewa ”kowane Dan’adam yana da ‘yancin da zaiyi zabe matukar yana da katin zabe”.

Barista Hassana Bashir ta bayyana hakan ne yayin ganawar ta da wakilin gidan rediyon Dala a ofishin ta.

Ta ce ”kowane dan’adam yana da ‘yancin yin zabe matukar yana da katin zabe”.

Ta kara da cewa, ”hatta dalibai da kuma wadanda ke zaune a gidan kaso, su na da ‘yancin yin zabe, tun da dai suma ‘yan kasa ne”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Barista Hassana Bashir ”ta kuma bukaci al’umma masu bin doka da oda yayin gudanar da zabe”.

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish