Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mota makare da kwaya da makamai.

Image may contain: 4 people, people smiling, people standing

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama wata babbar mota, makare da miyagun kwayoyi sama da kala 10, da kuma duro 12 na madarar sukudayin.

Kwamishinan yansanda na kano CP Muhammad Wakili, shi ne yayi holin matasan da kayayyakin miyagun kwayoyin da aka kama a yammacin jiya.

CP Wakili ya kuma ce, ”Rundunar ta kama wani mutum da wukake buhu biyar, sai kuma wasu matasa uku da aka kama da bindiga”.

Ya kara da cewa, ”Rundunar ta kuma saka dambar yaki da dilolin miyagun kwayoyi a fadin jihar nan”.

en_USEnglish
en_USEnglish