An ja hankalin al’umma da su rinka karanta alqur’ani mai girma.

Limamin Masallacin juma’a na Usman bin Affan dake unguwar Gadon Kaya, malam Abdallah Usman Gadon kaya, ya ja hankalin al’umma da su rinka baiwa karatun alqur’ani muhimmanci.

Malam Abdallah Gadon kaya ya yi wannan jan hankalin ne, jim kadan bayan kammala shirin rayuwa abar koyi na nan gidan rediyon Dala.

Ya ce ”sau da dama al’umma su kan yi watsi da karatun alqur’ani duk da muhimmancin da yake dashi”.

Ya kuma ja hankalin al’umma ”da su rinka koyon harshen larabci, maimakon mayar da hankali akan iya yaren turanci”.

Malam Abdallah Gadon kaya, ya kuma yi kira dalibai ”da su zage damtse wajen neman ilimin addini musamman na alqur’ani mai girma”.

en_USEnglish
en_USEnglish