Wasu ‘yan fashi sun shiga hannun ‘yan unguwa.

Image may contain: one or more people and people standing

Mai unguwar yankin Jakada dake karamar hukumar Gwale anan Kano, Malam Sani Sa’idu, ya bukaci al’umma da su rinka sanya idanu a yankunan su, domin gudun shigowar bata gari.
Sani Sa’idu ya bayyana hakan ne, yayin da al’ummar yankin unguwar jakada su ka samu nasarar kama wasu matasa biyu dauke da bindiga samfarin Pistol bayan da suka biyo wani mutum a motar sa a daren jiya.
Ya ce lokacin da abin ya faru baya gida, daga bisani aka sanar da shi, inda kuma nan take ya sanar da hukumar ‘yan sanda abin da ke faruwa.

Ya kuma ce rundunar ‘yan sanda ta yabawa al’ummar yankin bisa namijin kokarin da sukayi wajen kama wadanda ake zargin.

Suma wasu da sukayi nasarar kama wadanda ake zargin sun bayyana yadda lamarin ya faru.

A yanzu haka dai wadanda ake zargi da yunkurin aikata fashin na hannun rundunar ‘yan sandan yankin Dorayi Babba, yayin da guda daga ciki tun a daren na jiya ya cika wandon sa da iska.

en_USEnglish
en_USEnglish