Takaitattun Labarai na yau 11-4-2018

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, ta yi kira ga maniyatan bana da su guji yada jita-jita tare da mai da hankali wurin halartar bita da kuma bin dokar kasar Nijeriya da Saudiyya.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito mana cewa, Shugaban hukumar jin dadin alhazan a nan Kano, Malam Muhammad Abba Dambatta ne yayi kiran a lokacin da hukumar ta fara gabatar da bitar alhazan a karo na farko.

A nasa jawabin sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi na biyu, ya umarci maniyatan da su rinka tutubar malaman bitar a kan duk wani abu da ya shige masu duhu tare da kare martabar kasar nan yayin da kuma bayan kammala aikin hajjin bana.

Kungiyar bunkasa ilimi da cigaban demokradiyya da samar da daidaito a zamantakewa, SEDSAC tayi kira ga masu ruwa da tsaki da suyi duk mai yuwa wajen samawa matasa ayyukan yi, domin ta hakane kadai za’a iya magance matsalolin da matasan ke fama da su.

Babban daraktan kungiyar kwamred Umar Hamisu Kofar Na’isa ya kuma ce ”shugabanni na da muhimmiyar rawar takawa akan cigaban rayuwar matasa ta kowane fanni”.

Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, Arc Ibrahim Garba Kabara, ya yi kira ga matuka Baburan adaidaita sahu, da su rinka tuki cikin nutsuwa tare da bin doka da oda.

Cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai, mai kunshe da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa, ta rawaito cewa, Ibrahim Garba Kabara, ya kuma ce ”hukumar KAROTA, za ta cigaba da mayar da hankali wurin kula da ayukan ta na kare rayukan al’umma a koda yaushe”.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish