Gobarar Kannywood: Yadda aka sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango

Gobarar Kannywood: Yadda aka sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango

Idan baku manta ba gobara ta kunno a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wadda aka faro tsakanin manyan jarumai kuma jagorori a masana’antar jarumi Ali Nuhu da kuma Jarumi Adam Zango.

Lamarin ya farone biyo bayan zargin da Adam A. Zango yayi na cewa yaran Ali Nuhu sun zageshi hakan ya sanya shi kuma yayi ramuwa wadda za’a iya cewa ramuwar gayya wanda hakan bai yiwa Jarumi Ali dadiba, hakan ya sanya shi maka Adam A. Zango a wata kotu dake unguwar Fagge a nan Kano.

Ana tsaka da wannan ne hadaddiyar kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa wato MOPPAN ta jagoranci yin sulhu a tsakaninsu kamar yadda jaridar Leadership ta rawaito.

Dattawan Kannywood sun jagoranci sulhu tsakanin Adam Zango da Ali Nuhu yau a birnin Kano, wanda ya kawo karshen cece kucen da ake tafkawa akan wannan batu.

Allah ya kyauta.

en_USEnglish
en_USEnglish