Labarai A Takaice na yau Juma’a 03 05 2019

10:54 Limamin masallacin juma’a na Usman Bin Affan dake Gadon Kaya, Dr Abdullah Usman Umar, ya ja hankalin al’umma da su kaucewa mumunar dabi’ar nan ta zuwa gidajen alfasha da sunan daure shaidan a duk lokacin watan Azumin Ramadan.

Dr Abdullah Usman, ya yi kiran ne jim kadan bayan kammala shirin Rayuwa Abar Koyi na gidan rediyon Dala, ya kuma yi kira ga al’umma musamman ma masu hali dasu kara kaimi wurin tallafawa masu karamin karfi a yayin Azumin watan Ramadan da za a shiga.

Shugaban tsarin nazarin darussa dake kwalejin Sa’adatu Rimi, Malam Mansur Sani Ayagi, ya yi kira ga iyaye da su rinka bibiyar karatun ‘ya’yan su wanda ta haka ne nan gaba za a son muhimmancin sa.

Yayin zantawarsa da wakilin mu Nasir Khalid Abubakar, Malam Mansur Sani Ayagi, ya ce har idan iyaye za su rinka bibiyar karatun ‘ya’yan su babu shakka nan gaba zasu ga alfanun sa a wurin ‘ya’yan nasu.

en_USEnglish
en_USEnglish