Diloli suna sayar da kwai akan farashi mai rahusa, amma basu da ikon tilastawa masu shago -Alhaji Aminu Adamu

Tsohon shugaban kungiyar masu kiwon kaji ta jihar kano kuma mai gidan gona a yanzu, Alh Aminu Adamu ya bayyana cewa diloli suna sayar da kwai akan farshi mai rahusa, sai dai basu da ikon tilastawa masu shaguna kan sai sun sayar da kwan da rahusar kamar yadda suka siyo.

Alhaji Aminu Adamu, ya bayyana hakanne a ganawarsu da gidan radio Dala yana mai cewa dilolin suna sayarwa da sauki ne sabo da yadda aka tara kwan sosai danufin azumi, amma kuma sai ya yi yawa kuma ba kudi a hannun jama’a.

en_USEnglish
en_USEnglish