Gwamnati ta shirya bitoci kan kasuwancin musulunci da na zamani -Malam Aminu Harbau

Shugaban tsangayar nazarin tattalin arziki da ke kwalejin Sa’adatu Rimi Malam Aminu Harbau, ya shawarci Gwamnati data rinka shirya bitoci na musamman ga ‘yan kasuwa a lokuta daban-daban domin wayar musu da kai kan abun daya shafi kasuwancin musulinci da kuma na zamani.

Malam Aminu Harbau,ya yi wannan janhankalin ne yayin ganawar sa da wakilin mu Nasir Khalid Abubakar , yana mai cewa rashin sanin kasuwancin ta fuskokin guda biyu shi ne ke jawo durkushewar harkokin kasuwanci a jiha dama kasa baki daya.

en_USEnglish
en_USEnglish