Hisbah ta bukaci masu sayar da kayan masarufi kan su daina suyarwa da al’umma kayan da zai cutar da lafiyarsu

Hukumar hisba ta bukaci masu sayar da kayan masarufi su kauracewa sayarwa da al’umma kayan da zasu cutar da lafiyarsu a wannan wata mai alfarma dama sauran lokuta.

kiran yafito ne tabakin kakakin hukumar Hisba dake nan kano, Malam Adamu Yahaya biyo bayan wasu lalatattun kayyayakin lemo da suka samu ana sayarwa da mutane wadanda wa’adin su yakare a yankin titin Ibrahim Tayo.

Kakakin ya kuma ce hukumar zata sa ido dan ganin sun kama wadanda suke shigo da kayyayakin da wa’adinsu ya kare tare da mikasu ga hukumar da take da alhakin hukunta masu irin wannan dabi’ar.

en_USEnglish
en_USEnglish