Yakamata dattawa su da gidauniyar tallafawa marayu a unguwanninsu -Alhaji Kabiru Isyaku

Shugaban kungiyar Ramadan trust iniciative mai rajin tallafawa marayu a watan ramadana, Alhaji Kabiru Isyaku, ya shawarci dattijai a unguwaninsu daban-daban da su samar da wata gidauniya don taimakawa marayu da marasa karfi da suke cikin unguwaninsu.

Shugaban ya bayyana hakanne a ganawarsu da gidan radiyon Dala yana mai cewa samar da irin wadan nan gidauniyoyi don taimakwa masu karamin karfi da marayu daga mawadatan yankin zai taimaka matuka wajen samar da kyakkawar fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu tare da kyautata zamantakewa a tsakaninsu.

en_USEnglish
en_USEnglish