Iyaye su gargadi ‘ya’yansu kan yin amfani da tashe wajen tayar da fitina ko kwace -‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ja hankalin iyayen yara da su gargadi ‘ya’yansu don kaucewa yin amfani da tashe wajen tayar da fitina ko kwace.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan, yayin ganawarsa da wakilinmu Abba Isah Muhammad yau a shelkwatar hukumar dake unguwar Bompai.

DSP. Kiyawa yace basu hana tashe ba tashin hankali suka hana.

Shin ko yaya kuke kallon wannan batun?

en_USEnglish
en_USEnglish