Kotu ta yankewa wani matashi daurin shekaru 4 babu tara saboda ya tserewa kotu

Kotun majistrate mai lamba goma sha hudu ta yankewa wani matashi hukuncin dauri shekaru uku babau zabin tara, sakamakon samunsa da laifin tserewa daga kotun lokacin da ake tsaka da karanta masa takardar tuhumar akan zargin fashi da makami dakuma kisan kai.

Gabanin yanke masa hukunci a jiya, mai shari’a Aminu Usman fagge ya tambaye shi ko ya yi nadamar aikata laifin? amma ya ce bai yi nadamarba inda kotun ta yake masa hukuncin nan take, ta kuma ce batun zargin fashi da makamin da kisan kai ana jiran shawarar lauyoyin gwamnati a kai.

en_USEnglish
en_USEnglish