‘Yan sanda sunyi holen ‘yan fashi da makami, fyade da masu satar motoci sama da mutum 50

Rundunar Yansandan jihar Kano tayi holen wasu mutane Fiye da hamsin da take zargin sun aikata laifukan Fashi da makami, fyade da kisan Kai Gami da Satar motoci.
Da yake holin muyanen a shalkwatar Rundunar dake Unguwar Bomfai a nan Kano a yau Alhamis, kwamishinan yansandan Kano CP Muhammad Wakili, ya nemi Karin hadinkai daga Yan kishin kasa Don Kara inganta Harkokin Tsoron rayuka da Dukiyar Al’umma.
A nasa jawabin Kakakin Rundunar Yansandan ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna, yace tuni sun gurfanar da wasu gaban kotu yayinda wasu ake cigaba da bincike.
Mun kuma Zanta da wasu cikin wadanda ake zargin ciki harda wata mata da ake zargin tana taimakawa mijinta Wajen aikata Fashi.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa Rundunar Yansandan na gargadi Iyaye su ja kunnen yaransu Don kaucewa tayar da fitina ko kwace yayin gudanar da Aladar Tashe.
Duba hotunan dake kasa:
en_USEnglish
en_USEnglish