Yawan shan ruwa loakcin sahur da buda baki yana magance ciwon koda

Wani kwararren likita Dakta Ibrahim Muhammad Badamasi dake asibitin koyarwa na malam Aminu Kano ya bayyana yawan shan ruwa a lokacin sahur da buda baki tare da kauracewa yawan gumi a matsayin rigakafin ciwon koda da kuma rage zafin ciwon ga wanda ke dauke da cutar.

A ganawarsu da gidan radiyon Dala, Dakta Ibrahim Muhammad Badamasi      ya ce yawan ruwa a jikin mutum taimaka wajen gudanawar sinadaran jini a jiki don taimaka aikin koda kamar yadda ya kamata, yana mai shawartar wadanda suke dauke da cutar da su ci gaba da ziyartar likita tare da kiyaye sharudan daya gindaya musu musamman a wannan wata na ramada dama sauran lokuta.

en_USEnglish
en_USEnglish