An fara sauraron shari’ar magidancin da ya kashe matarsa a Kano

Mutumin Nan Aminu Inuwa wadda ake tuhuma da hallaka matarsa ya kuma bunneta cikin dare a gidansa dake unguwar dorayi a karamar hukumar gwale, ya ce bai gamsu da lauyan da zai kare shiba a kan shari’ar da za’a yi masa a gaban babbar kotun jiha.

Andai gurfanar da Aminu Inuwa a gaban babbar kotu mai lamba 8 karkashin justice Usman Na’abba inda lauyan gwamnati barista lamido sorondinki ya gabatar da shedu biyar don tabbatar da laifin akan wanda ake zargi kasancear ya musa laifin tunda farko, saidai rashin gam,suwa da lauyan da zai kare shi ya sanya aka dage shari’ar zuwa ranara sha-daya da watan gobe.

en_USEnglish
en_USEnglish