Musulmai su dage wajen fito da kyawawan halayen musulunci -Farfesa Salisu Shehu

Babban sakataren zartarwar cibiyar inuwar musulmin Nigeria, farfesa Salisu Shehu, ya shawarci musulmai a kasar nan da su kara zage dantse wajen fito da kyawawan dabi’un musulinci a aikace, musamman a wanna wata na Ramadan dama sauran lokuta, don kara fito da kyawun musulinci da kuma inganta alakar musulincin da sauran addinai a Nigeria.

Farfesan ya yi wanan jan hankalinne da safiyar yau, a ganawarsu da gidan Radion Dala, kan batun wani gangamin lakcar shekara-shekara da kungiyar zata gabatar a wannan wata mai taken inganta tarbiyar musulmai a zamantakewar yau da kullum da kuma cikin gidajen aure.

en_USEnglish
en_USEnglish