Wani matashi ya hallaka wani akan naira ashirin

Babbar kotun jiha mai lamba goma sha hudu karkashin justice Dije Abdu Aboki ta sanya ranar sha-hudu ga watan gobe, don yin hukunci kan wata shari’a da aka gurfanar da wani matashi Umar ya kubu wanda ake zarkin ya hallaka wani Muhammad Ibrahim Gandu a kan kudi naira ashirin.

A zaman shari’ar wanda ya gudana a jiya, lauyan gwamnati barista lamido sorondinki ya gabatar da shedu biyar,  a yayinda shi kuma wanda ake zargin ya kare kansa, inda daga bisani kotun ta sanya ranar ta 14 ga watan goben don yin hukuncin.

en_USEnglish
en_USEnglish