Akwai bukatar hukumomi su maida hankali wajen tallafawa marayu -Dr. Nura Abdullahi

Gidauniyar Kairat Islamic Trust dake tallafawa mabukata, ta bukaci hukumomi da gwamnonin jihohin kasar nan da su rinka tallafawa marayu da masu karamin karfi da irin kayan da gwamnati ke kwacewa mai makon Konawa.

Daraktan gidauniyar, Muhammad Nura Abdullahi, ya yi kiran ne lokacin da gidauniyar ta ke raba tallafin shinkafa da atamfofi ga iyayen marayu 500 da suka amfana a Kano.

en_USEnglish
en_USEnglish