Muna rokon gwamnati ta samar mana da ruwan sha -al’ummar Tudun Rubudi

Al’ummar yankin Kurna layin gidan Kara da Tudun Rubudi dake nan Kano, sun yi kira ga gwamnatin jiha da ta sama masu ruwan sha a yankunan su.

Mazauna yankin sun yi wannan kiran ne biyo bayan da masu siyar da ruwa a yankin wato ‘yan garuwa suka tsinduma yajin aiki, sun kuma roki gwamnati da ta shigo cikin lamarin don sama masu ruwan sha da tituna a yankunan su.

en_USEnglish
en_USEnglish